"Duniya ta gaza kan taimakon 'yan Syria"

Image caption An shafe tsawon lokaci ana rikici a Syria

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah-wa-dai da gazawar kasashen duniya wajen kare dubban 'yan gudun hijirar da ke tserewa daga Syria.

Shugaban hukumar bincike na majalisar Paulo Sergio Pinheiro, ya ce ya zama wajibi al'ummomin duniya su yi abin da ya dace bisa tausayi domin inganta hanyoyin da doka ta amince da su don yin hijira.

A cikin rahoton da 'yan tawagarsa suka gabatar, Mista Pinheiro ya yi gargadi cewa yakin Syria zai iya ci gaba na tsawon shekaru, ta hanyar take hakki kamar tayar da bama-bamai da kisan gilla da lalata dukiyar kasa da kuma fyade.

An kwashe tsawon shekaru ana fama da rikici a Syria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare kuma da raba miliyoyin mutane da muhallansu.