Boko Haram ta raba mutane miliyan biyu da muhallinsu

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Video
Image caption Sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon ayyukan Boko Haram.

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, IOM ta ce sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallansu a arewa maso gabashin Nigeria sakamakon ayyukan 'yan Boko Haram.

Hukumar IOM ta ce ta sake nazari kididdigar da ta yi a baya ne, inda ta ce mutane miliyan daya ne suka rasa wurin zama dalilin hare-haren Boko Haram.

Hakan na zuwa bayan da alamu ke nuna cewar rundunar sojin Nigeria na samun galaba a kan mayakan Boko Haram.

Ko a cikin wannan makon ma, sai da rundunar sojin saman kasar ta yi ikirarin cewa ta yi luguden wuta a kan wuraren da 'yan Boko Haram suka boye a dajin Sambisa.

Dubban mutane aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rikicin Boko Haram a cikin shekaru shida a Nigeria