An soki gwamnan jihar Kaduna

Image caption Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufai

Wata kungiyar farar hula ta soki gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufai a kan matakan da ya ke dauka a cikin jihar.

Kungiyar ta CEDRA ta soki matakin rushe wasu gidaje da kuma korar manyan sakatarorin gwamnati da kuma tantance ma'aikata tare da nade naden mukamai.

Sai dai ta ce wa'adin da aka debar wa mutane a kan su tashi daga gidajesu ba dai dai ba ne musamman idan anyi la'akari da halin da kasar ta ke ciki.

Kungiyar ta kaddamar da littafi da ke bayani a kan matakan da Nasiru El Rufai ya dauka a kwanaki 100 da ya karbi ragamar mulki a jihar Kaduna.

A baya dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta aiwatar da aikin rushe gidaje da sauran wurare da aka gina ba bisa ka'ida ba a filaye mallakar gwamnati.