'Yan ci-rani 40 sun nitse a tekun Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daruruwan 'yan ci-rani sun rasu a cikin teku a bana

Hukumar sa ido a kan kaurar jama'a IMO ta ce 'yan ci-rani da suka kai arba'in sun salwanta bayan jirgin ruwan da suke ciki ya nitse a gabar tekun Libya.

Kakakin hukumar ya ce, dakarun ruwan Italiya sun ceto wasu da suke cikin jirgin ruwan, kana aka kai su tsibirin Lampedusa.

Daga cikin wadanda aka ceto akwai wata mace 'yar Nigeria da ta haihu a kan hanya.

Jirgin ruwan ya lalace ne jim kadan da barin gabar teku.

Hakan na zuwa ne bayan an yi jana'izar yaron da mutuwarsa ta sake jawo hankali ga batun 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani musamman daga Syria da ke neman mafaka a kasashen Turai.