Shugaban Nijar ya yi wa gwamnatinsa garanbawul

Image caption Shugaba Muhammadu Isufu na jamhuriyar Nijar

Shugaba Muhammadou Isufu na jamhuriyar Nijar ya yi wa gwamnatinsa garambawul a ranar Alhamis, inda ya sauke ministan ma'aikatar raya karkara Dr Amadu Bubakar Sise.

Kazalika, ya kuma sauke Ministan raya al'adu na kasar Malam Usman Abduda wanda yake jam'iya daya da Amadu Bubakar Sise.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta yi wani karin haske ba dangane da dalilan garambawul din, amma a can baya rahotanni sun sha ambato cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Dr Amadu Bubakar Sise da shugaba Muhammadou Isufu.

Dr Amadu Bubakar Sise dai shi ne shugaban jam'iyar UDR, daya daga cikin jam'iyun da suka taimakawa Mahamadu Isufu ya ci zabe a 2011.