Ana muhawara a kan #ZamanAure

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ana fafata muhawarar kan zaman aure a shafin Twitter.

Wata muhawara ta mamaye dandalin sada zumunta na Twitter a Najeriya, a kan yadda zaman aure a kasar Hausa ya kamata ya kasance.

Wani shafin Twitter mai suna @Bahaushee ne ya kirkiro da maudu'i mai taken #ZamanAure a ranar Juma'a, inda ya ja hankalin Hausawa musamman matasa maza da mata inda suka ta tafka muhawara kan yadda zaman aure yake a wannan zamanin.

Abin sha'awa dangane da wannan muhawara shi ne, yadda mutane suka yi amfani da damar wajen fito da matsalolin aure da kalubalen da ma'aurata suke fuskanta da kuma yadda za a magance su.

Matsalolin da aka tattauna a kai sun hada da yawan mutuwar aure, da yadda ake kashe makudan kudi tun daga neman aure zuwa biki wanda hakan ke firgita matasa da dama, da kuma yadda Bahaushe yake aure-aure.

Wasu da dama kuma kira suka yi cewa idan Hausawa suka daina cakuda al'ada da addini, suka kuma daina kwaikwayon al'adun da ba nasu ba a cikin neman aure da zamantakewarsa, to hakika za a samar da al'umma mai kima irin wacce ake fatan gani.

A Najeriya dai ana amfani da shafukan sada zumunta domin tattauna al'amura da dama masu ma'ana, amma a wasu lokutan abin ba haka yake ba.