Austria za ta kwaso karin 'yan hijira

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijra

Hukumomin kasar Austria sun ce za a samar da karin jiragen kasa da zasu ci gaba da jigilar 'yan gudun hijira da suka shafe kwanaki suna makale a kasar Hungary.

Akalla 'yan hijira dubu 10 ne ake tsammanin sun shiga Austria a jiya Asabar, yayin da da dama daga cikin su suke wucewa kasar Jamus.

Austria ta yanke shawarar tura karin jiragen kasar Hungary domin jigilar 'yan gudun hijirar da suka makale a can akan hanyar su ta shiga wasu kasashen Turai, bayan gwamnatin Hungary ta ce ba zata bada karin motocin safa na bus ba domin ci gaba da jigilar su.

Gwamnatin Jamus ta ce sassaucin da aka yi na wucin gadi ga dokar yin kaura ta tarayyar turai, ya taimaka wajen kaucewa fada wa wani mummunan yana yi na bukatar agajin jinkai a bakin iyakar Hungary da Austria.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel zata gana da wasu shugabannin da aniyarsu tazo daya a Tarayyar Turai domin tattauna shirin magance matsalar.