'Yan gudun hijira sun fara isa Austria

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption 'Yan gudun hijira daga Syria

'Yan gudun hijira da za a fidda su daga kasar Hungary sun fara isa kasar Austria inda jami'an kungiyar kungiyar Red Cross suka yi musu tarba mai kyau a wani sansani.

Rahotanni sun ce 'yan gudun hijirar da aka tarba da mutuntawa a Austria, suna cikin gajiya da kuma farin ciki.

Motocin safa da dama ne a kasar Hungary suke jigilar dubban 'yan gudun hijirar zuwa Austria, bayan Austria da Jamus sun amince su karbi dubban 'yan gudun hijirar da suke so su fara sabuwar rayuwa a yammacin Turai.

'Yan gudun hijirar da suka fara isa Austria, sun karasa ne da kafa, bayan motocin safan sun ajiye su a bakin iyakar kasar daga Hungary.

Wasu daga cikin su suna dangeshi, amma da daman su suna murmushi na samun sauki.

Jami'an kungiyar agaji ta Red Cross sun tarbe su da barguna da kuma shayi.

Kimanin 'yan gudun hijirar 800 zuwa 3000 ne ake sa ran zasu isa kasar ta Australia a cikin sa'o'i masu zuwa.