Facebook ya bullo da manhajar karatu ta yara

Image caption Masu amfani da shafin Facebook

Shafin sada zumunta na Facebook ya bullo da wata manhaja ta karatu da za ta bai wa yara damar koyon karatu da kadan-kadan.

Shafin ya ce yana aiki tare da makarantun Summit Public Schools wadanda suka fara amfani da tsarin koyarwar da ke bai wa dalibai damar yin karatu ta intanet sannan a rika gyara musu a a cikin aji.

Shafin na Facebook ya ce an raba manhajar da sauran tsare-tsaren sada zumunta na shafin.

Sai dai wasu na dari-darin wannan sabon tsari da shafin ya bullo da shi.

Wani babban jami'in shafin Chris Cox ya ce Facebook yana so ya samar da aji dai-dai da bukatun dalibai.

Shafin ya ce tsarin zai bada dama a gwada dalibai ta intanet, yayin da malamai zasu yi amfani da lokutan aji domin yin tushin abinda dalibai suka karanata ta intanet.