Za'a takaita gudun mota a Nigeria

Image caption Motocin sufuri a Najeria

A Najeriya, a kokarin rage hadurra a hanyoyin mota a kasar, hukumar kiyaye hadurra ta kasar- Federal Road Safety Commission ta fara wayar da kan direbobi game da amfani da wata na'ura mai rage gudun mota a titinan kasar.

Hukumar ta ce za a makala na'urar ce a jikin mota domin katse hanzarin dukkan wani direba da ke kokarin sharara gudu da ya wuce misali.

Tafiyar kilomita 100 a sa'a daya ne adadin gudun da aka kayyade wa mota a Najeriya, to amma direbobi da dama a kasar kan zarta haka, abin da a wasu lokutan ke haifar da munanan hadurran mota.

Wani jami'in hukumar kiyaye haduran, Abdullahi Aliyu ya ce idan aka fara amfani da na'urar, kananan motoci zasu rika tafiya a 100 bisa ma'unin gudun mota, motocin safa na bus za su rika tafiya a 90, manyan motoci kuma a 90.

Sai dai wasu daga cikin direbobin da suka halarci taron wayar da kan sun koka da tsadar na'urar, inda suka yi kira ga gwamnati data raba musu ita a kyauta.