Dubban 'yan gudun hijira sun isa Jamus

Wasu yan gudun hijira da suka isa Jamus
Image caption Wasu yan gudun hijira da suka isa Jamus

'Yan gudun hijirar sun shiga kasashen biyu ne ta Hungary bayan hukumomin kasar sun dan daga kafa ga 'yan gudun hijirar dangane da tafiye-tafiye.

Masu aikin agaji sun yi musu kyakyawar tarba inda daga nan wasunsu suka wuce zuwa birnin Vienna, wasu kuma suka dunguma zuwa birnin Munich dake kudancin Jamus.

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar da suka isa Jamus yace sun yi tafiya mai hadari daga inda suka taso inda suka bi ta kasashe da dama amma sun yi murnar isar su kasar Jamus.

Wasu jama'ar a Jamus sun yi maraba da 'yan gudun hijirar inda suka rika baiwa yara Alawa da kuma abubuwan wasa.