Al Shabaab ta kwace wasu garuruwa a Somalia

Mayakan kungiyar al Shabaab
Image caption Mayakan kungiyar al Shabaab

A baya dai akwai sansanonin dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka wato AMISOM a wadannan garuruwa, amma suka janye bayan harin da 'yan Al Shabaab suka kaiwa dakarunsu a sansaninsu dake garin Janale.

An dai kawar da kungiyar Al Shabaab daga Mogadishu, babban birnin kasar, amma suna cigaba da yakin sunkuru a mafi yawancin kudancin Somaliyar.