Paparoma: A taimakawa 'yan gudun hijira

Paparoma Francis shugaban katolika na duniya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Paparoma Francis shugaban katolika na duniya

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci mabiya darikar Katolika a nahiyar turai su bada gudunmawar su wajen taimakawa yan gudu hijirar.

Dubban 'yan gudun hijirar dai suna kan hanyarsu ta zuwa Austria da Jamus bayan sun kwashe kwanaki cikin tsaka mai wuya a Hungary

Ana kuma daukar wasu daruruwa a motoci daga kan iyakar Austria da Hungary, wasu da dama kuma sun shigo jirgi daga birnin Budapest.

Hakannan kuma jerin gwanon motoci kusan dari da hamsin na masu aikin sa kai na Austria sun tsallaka cikin Hungary domin debo karin wasu 'yan ciranin:

Ko da a ranar Asabar kadai an bada rahotannin cewa, 'yan gudun hijira fiye da dubu goma ne suka shiga Austria.

A biranen Jamus da dama mutane sun yi tururuwa a tashoshin jiragen kasa inda suka rika yin marhabun ga 'yan gudun hirar.