Buhari ya cika kwana 100 a kan mulki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya cika kwanaki 100 a kan karaga

A ranar Lahadi nan ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yake cika kwanaki 100 akan karagar shugabancin kasar.

Buharin dai ya sha rantsuwar kama aiki ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015.

Bisa al'adar kasar, kwanaki darin lokaci ne da 'yan kasar suke yi wa gwamnati hisabi kan irin ci gaba da aka samu ko akasin hakan, a tsawon lokacin.

Sai dai kuma wasu na da ra'ayin cewa yi wa gwamnati hisabi a kwanaki 100 al'ada ce da aka aro daga Amurka saboda haka ba ta da hujja bare makama.

Haka kuma, jami'an gwamnatin kasar sun ce shugaban bai sha alwashin yin wani abu ba a cikin kwanaki darin.

Yayin da ake wannan takaddama, wasu daga cikin 'yan kasar suna yin alasan barka dangane da yadda sha'anin tsaro da rashawa da cin hanci suka inganta, wasu na da ra'ayin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba, a kwanaki darin farko na shugaban.