An kama mai jirgi mara matukin da ya fado

Image caption Jirgi mara matuki

An kama wani malamin makaranta a New York saboda ya lula wani karamin jirgi mara matuki daya fado a wurin da 'yan kallo ke zama a gasar kwallon Tennis ta US Open.

An tuhumi mutumin mai suna Daniel Verley dan shekaru 26 da gangancin lulawa da jirgin a wurin da jama'a ke taruwa, abin da ya sabawa doka.

Jami'an gudanar da gasar ta Tennis sun ce babu wanda ya samu rauni sakamakon fadowar da jirgin ya yi, amma dai rikitowar jirgin ta kawo tsaiko a gasar.

Lamarin ya faru ne a filin wasa na Louis Armstrong.

Daya daga cikin 'yan wasan Flavia Pennetta ta bayyana cewa ta razana sosai data ji karar jirgin da kuma faduwar sa.

Ta ce babu wanda ya fada musu cewa abin da ke lulawa jirgi ne, sannan kuma ya tarwatse da ya fado kasa.

Acewar ta, inda jirgin ya fado kan 'yan kallo, to da yayi mummunar barna.

An taba kama wani mutumin birnin na New York a bara lokacin da ya lula wani jirgin mara matuki a wajen filin da ake gasar Tennis, lokacin da Ms Pennetta na buga wasa da Serena Williams.