Biritaniya za ta dauki 'yan gudun hijira 20,000

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria na cikin tsaka mai wuya

Biritaniya ta ce za ta samar wa 'yan gudun hijira daga kasar Syria su dubu ashiri da matsugunai nan da shekaru biyar masu zuwa.

Firai ministan Biritaniya, David Cameron, wanda ya sanar da haka a jawabinsa ga majalisar dokokin, ya ce za a debi 'yan gudun hijirar ne daga sansanoni da ke Turkiya da kuma sauran kasashe makwabta domin su daina kokarin tafiyar nan mai hadarin gaske zuwa Turai.

Kwamishinan hukumar Turai a kan kaurar jama'a, Dimitris Avramopoulos, ya ce tayin samar da mafaka da aka yi wa mabukata haki ne da ya rataya a kan wuyan kowa.

Gwamnatin Denmark ta wallafa talla a jaridun kasar Lebanon inda ta gargadi 'yan ci-rani masu anniyar ketarawa a kan kada su taho Denmark saboda za ta bullo da sabbin ka'idoji masu tsauri.

A kasar Faransa kuwa, shugaba Francois Hollande ya ce shi da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel sun amince da wani shiri da zai tilastawa kasashen Turai rarraba 'yan gudun hijira tsakaninsu.