Buhari ya gana da Mahama a Accra

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Ghana da Nigeria sun dade suna hudda a tare

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya isa Accra, babban birnin kasar Ghana domin tattaunawa da shugaba John Mahama.

Ganawar za ta mai da hankali ne a kan yaukaka dangataka tsakanin kasashen biyu, wadanda suka dade suna hulda da juna.

Shugaba Buharin ya sauka a birnin Accra ne tare da mai ba shi shawara kan harakokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da kuma wasu manyan jami'an gwamnati.

Batun tsaro na daga cikin abubuwan da za su tattauna, musamman kalubalen da ake fuskanta a wasu kasashen yammacin Afrika sakamakon rikicin Boko Haram.

Tun bayan hawansa karagar mulki, shugaba Buhari ya kai ziyara wasu makwabtan kasashe kamar Nijar da Kamaru da kuma Chadi domin hada hannu wajen murkushe 'yan Boko Haram.