Ambaliya ta yi barna a Saliyo

Image caption Abubuwa sun tsaya ciki a Saliyo

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar Saliyo ya janyo ambaliya ruwa abin da ya kai ga ruftawar gidaje da manyan hanyoyi.

Hukumomi a kudancin lardin Bo, sun shaida wa BBC cewar ambaliyar ta lalata gidaje fiye da 70 a daya daga cikin yankunan sannan kuma daruruwan mutane sun rasa muhallansu.

A halin yanzu dai hanyar da ta hada lardin Kenema da sauran yankunan kasar ta kasance male-male a cikin ruwa.

Lamarin ya jefe kuncin rayuwa kan dubban matafiya wadanda suka makale a wasu yankunan kudancin Saliyo.