Za a rage ofisoshin jakadancin Nigeria — Buhari

Buhari
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai daukaka ofisoshin jakandancin Najeriya da ke kasashen waje.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta rage ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje.

Shugaban ya ce nan ba da jimawa ba za a kafa kwamiti na musamman domin yin aikin tantancewa kan ofisoshin ta yadda za a daga martabar ofisoshin jakadancin don su yi aiki yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne bayan da babban Sakatare a ma'aikatar kula da hulda da kasashen waje na kasar ya yi masa jawabi a kan ayyukan ma'aikatarsa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa lokacin fuskantar gaskiya ya yi.

Najeriya ba za ta ci gaba da aiki da ofisoshin jakadancin da babu kayan aiki ba da kuma ma'aikatan da sha'awarsu ga aiki ya yi rauni ba.