Watakila a haramta kayan abincin Nigeria a Turai

Image caption Shagon sayar da kayan abincin Nigeria a London

Hukumar Tarayyar Turai ta yi barazanar haramta shigar da kayayyakin abinci na Nigeria zuwa cikin kasashensu.

Hukumar ta ce za ta dauki matakin ne idan har yawan maganin kashe kwari da ake sawa ya kai minzalin cutar da bil adama.

Ana zuba maganin kashe kwarin da yawansa ya wuce kima a wasu kayayyakin abincin da ake fitar wa daga Nigeria zuwa kasashen Turai.

Tuni aka gano adadin maganin kashe kwarin da ya wuce kima a busashen kifi da nama da gwada da dankali da agushi da kuma wasu abincin da ake shigar da su cikin Turai daga Nigeria.

A watannin da suka wuce ne aka haramta shigar da waken Nigeria a kasashen Turai.