Kotu ta yi watsi da bukatar Gbagbo

Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo

Alkalai a kotun hukunta miyagun laifuka ta duniya sun yi watsi da bukatar da tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya shigar inda ya nemi ayi ma sa sakin wucin gadi domin ya duba lafiyarsa.

Ana tuhumar Mr Gbagbo mai shekaru 70, da aikata laifukan yaki.

A watan Nuwamba ne za a soma yi masa sharia .

Ana tuhumar Mr Gbagbao da aikata laifi bayan da ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da aka yi a shekara ta 2010.

Mutane sama da dubu 3 aka kashe a tashin hankalin da ya biyo baya.