Ana bikin ranar yaki da jahilci

Wasu   yan makaranta a Najeruya Hakkin mallakar hoto
Image caption Dalibai na daukar darasi a wata makaranta a Najeriya

A ranar Talata takwas ga watan Satumba ne ake gudanar da ranar yaki da jahilci na bana.

Rana ce da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da kuma al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta kebe domin yaki da jahilci a duniya.

An dai kebe ranar ce domin nuna muhimmancin ilimi a tsakanin al'umma baki daya, kuma an fara gudanar da bikin zagayowar wannan ranar a shekarar 1965.

Sai dai masana a fannin ilimi a Najeriya na cewa batun yaki da jahilci na fuskantar kalubale a yankin arewa maso gabashin kasar musamman a jihohin da ke fama da tashe-tashen hankula na mayakan kungiyar Boko Haram, inda ilimin yara ke cikin matsala.

Taken ranar ta bana ita ce inganta ilimin da zai yi tasiri a kan ci gaban al'umma