Buhari ya gana da Obasanjo a Aso Rock

Hakkin mallakar hoto STATE HOUSE
Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Obasanjo ya kai wa Buhari ziyara tun da Buhari ya zama shugaban Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo, fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Cif Obasanjo ya ki amsa tambayoyin da 'yan jarida suka yi masa a kan makasudin ziyarar da kuma abin da suka tattauna, yana mai cewa cikin raha da harshen yarbanci 'komot joo'; ma'ana "ku gafara ku ba ni wuri."

Ganawar da shugabannin biyu suka yi ta kimanin sa'a guda ta ja hankalin manema labarai a kan makasudin ziyarar tsohon shugaban na Najeriya a wannan karon.

Masu lura da al'amura dai na ganin cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da al'amuran da suka shafi kasar ba.

A ranar 20 ga watan Agustan da ya wuce ne shugaba Buhari ya nada Cif Obasanjo a matsayin wakilinsa na musamman mai shiga tsakani a rikicin da ke ruruwa a Guinea Bissau.