Sojojin Kamaru sun yi zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru na cikin masu yaki da Boko Haram

Wasu sojojin Kamaru da suka yi aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen waje sun gudanar da zanga-zangar lumana a Yaounde domin matsa wa hukumomi su biya su hakkokinsu.

Sojojin wadanda suka yi aiki a Jamhuriyar tsakiyar Afrika a lokacin da tashin hankali ya mamaye kasar, sun yi jerin gwano ne daga ofishin Firai minista zuwa ma'aikatar tsaro, suna neman kungiyar hadin kan Afrika watau AU ta biyasu hakkokinsu na tsawon shekaru biyun da suka yi aiki a kasar waje.

Wasu majiyoyi sun ambato sojojin suna cewa duk da shigar da korafe-korafensu a gaban ma'aikatar tsaro, da kuma ganawar da suka yi da ministan tsaro har a yanzu ba su samu bayanai masu gamsarwa ba game da matsayinsu.

A kan haka ne suka yanke shawarar yin zanga-zangar

Hakan ya kai ga rufe wasu manyan tituna a birnin Yaounde da kuma takaita zirga-zirgar ababen hawa.

Ana sa ran cewa kakakin gwamnatin Kamaru, Issa Tchiroma Bakary zai yi wa manema labarai bayanai kan wannan batun.