An daɓa wa alkalai wuka a China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana yawan yanke hukuncin kisa a kotunan China

Wani mutum a China ya daba wa wasu alkalai uku wuka, yayin da ake sauraran wata shari'a a kan kwadago.

Daya daga cikin alkalan a lardin Hubei ya samu munanan raunuka.

Masu aiko da rahotanni sun ce a 'yan kwanakin nan ana samun karuwar kai wa mutane hare-hare.

Sai dai kuma ba'a cika samun manyan rikice-rikice ba a China.