Tarihin da Sarauniya Elizabeth ta kafa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarauniya Elizabeth ta kafa tarihi

Jama'a a yankin Scotland sun yi wa sarauniya Elizabeth tafi da sowwa a ranar da ta zamo basarakiyar da ta fi dadewa a kan gadon sarautar Biritaniya.

Ta wuce kakar-kakarta, Sarauniya Victoria, wadda ta yi shekaru sittin da uku da wata bakwai da kwanaki biyu.

Da take bude wani sabon layin dogo a yankin Scotland, Saurauniyar ta ce bata taba tsammanin za ta kawo wannan lokacin ba a kan sarautar kuma ta gode wa kowa a kan sakonnin taya murna masu sosai rai da su ka aika mata.

A majalisar dokokin Biritaniya, Firai minista David Cameron ya jagoranci jawabai a kan sarauniya Elizabeth, yana cewa ta jagoranci kasar cikin girma da arziki da martaba.

An daga gadar Tower bridge domin faretin jiragen ruwa a kan kogin Thames dan girmama Sarauniyar a London.