Ghana: Za a binciki alƙalai

Hakkin mallakar hoto Getty

Majalisar alƙalai ta Ghana za ta soma gudanar da bincike a kan cin hanci da rashawa da wani ɗan jarida ya bankaɗo tsawon shekaru biyu.

Ana zargin sama da alƙalai talatin da karɓar cin hanci da yi wa mutane barazana dan su ba su kuɗi.

Ɗan jaridar mai suna, Anas Aremeyaw Anas ya ce, yana da shaidar hoton bidiyo na kusan tsawon sa'o'i ɗari biyar da ya miƙawa babban mai shari'a na ƙasar.

An kira alƙalan domin su bayyana a gaban majalisar alƙalai ranar alhamis.

Kawo yanzu dai ba wanda ya ce uffan dangane da zarge zargen.