Turai za ta yi nazari a kan 'yan cirani

Image caption 'Yan gudun hijira

Nan ba da jimawa ba ne Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean Claude Juncker zai fitar da sabon shiri na yadda za a tunkari matsalar yawan 'yan ciranin da ke kwarara cikin nahiyar Turai.

Zai bayar da cikakken bayani na shawarwarin yadda za a tsugunar da 'yan cirani 60,000, wadanda a baya-bayan nan suka isa kasashen Girka da Italiya da Hungary, a daukacin kasashen Turai guda ashirin da biyu.

Za kuma a gabatar da shawarwarin da za su tilasta wa kasashen Turai rarraba 'yan gudun hijira tsakaninsu a nan gaba, idan har aka shiga wani yanayi na gaggawa.

Ana kuma tsammanin Mr Juncker zai yi kira da a kafa wani asusu na miliyoyin Euro, domin taimakawa kasashen Afirka rage yawan mutanen da ke tunkarar nahiyar ta Turai.