Microsoft na fafatawa da gwamnatin Amurka

Image caption Microsoft

Miscrosoft zai koma kotu domin ci gaba da rikicin da yake game da bukatar gwamnatin Amurka na cewa ya mika wasu sakonnin email da yake ajjiye da su a wata cibiyar tattara bayanai dake kasar Ireland

A shekarar 2014, wata kotu ta yanke hukuncin da ya goyi bayan ikirarin da gwamnatin Amurka ta yi na cewa saboda tana da hurumi akan kamfanin dake da ofis a Amurkar, za ta iya tilasta masa mika mata bayanan da yake da iko da su ko da ace a wata kasar ake ajjiye da su

Amma kamfanin Microsoft ya bada shawarar cewa hakan ya sabawa dokokin sirri

A madadin haka kamfanin ya ce dole ne Amurkata mutunta 'yancin wasu kasashensannan kuma ya nuna alamun cewa Washington ta yi amfgani da yarjejeniyar taimakon Alkalai idan har tana son samun sukunin wadannan bayanai daga kasar Irelans da kuma wasu cibiyoyin tattara bayanai dake wajen Amurkar

Tuni kasar Ireland ta ce ta na duba wannan bukata cikin gaggawa

Wannan sain-sa zai nuna karfin da Amurka ke da shi a kan kamfanonin dake cikin kasar.