An samu raguwar mace-macen kananan yara

wasu yara kanana da iyayensu
Image caption wasu yara kanana da iyayensu

Majalisar Dinkin Duniya da kuma Hukumar lafiya ta duniya sun ce a an samu gagarumar nasara wajen rage yawan mutuwar kananan yara a duniya.

Wani rahoton da suka fitar ya ce mutuwar da kananan yara kan yi ta ragu da sama da rabin adadin wadanda ke mutuwa a cikin shekaru 25 din da suka wuce.

Rahoton ya ce a bana ma ana sa ran cewa adadin yaran da ke mutuwa zai ragu sosai zuwa kasa da miliyon shida.

Amma rahoton ya ce har yanzu kasashe matalauta da ke kuda da sahara na fuskantar kalubale wajen rage mutuwar kananan yaran.