Malaman Islamiyya za su sha dauri a Ingila

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mohammed Waqar (hagu) da Mohammed Siddique (dama)

Wata kotu a Biritaniya ta yanke wa wasu malaman Islamiyya biyu hukuncin daurin shekara daya a kurkuku saboda laifin dukan wani yaro mai shekaru 10 da bulala saboda ya yi kuskure a karantun Kur'ani.

Mohammed Siddique mai shekaru 60, da dansa Mohammed Waqar mai shekaru 24 sun amsa laifin cin zalin yaro dan kasa da shekaru 16.

Sun buge yaron har sau hudu a masallacin Jamia na unguwar Sparkbrook da ke Birmingham a Ingila tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2014.

Mai shigar da kara na gwamnati, Sam Forsyth ya ce malaman Islamiyyar sun duke yaron da bulalar roba sannan kuma sun mare shi a cikin aji.

Malaman sun duke yaron sau hudu a lokuta daban-daban, kuma akwai hotunan da ke nuna shaidar bulala a kafarsa.

Lauyan da ke kare malaman, Charanjit Jutla ya ce malaman, mutanen kirki ne kuma sun yi nadamar abin da suka yi.

Sai dai alkalin kotun a Birmingham Mark Wall ya ce "ba za a laminci zalunci ba musamman bugu da sanda."

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Masallacin da malaman suke koyar da dalibai a Birmingham