"Sambarka da kwana 100 na Buhari"

Hakkin mallakar hoto Bauchi Facebook Page
Image caption Sheikh Dahiru Bauchi na daga cikin manyan Shehunnan darikar Tijjaniyya.

Wani Malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yabawa kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari a kwanaki 100 na mulkinsa

A hirar da ya yi da BBC, Malamin ya ce babbar nasarar da aka samu shi ne dakile ayyukan 'yan Boko Haram a inda yanzu sojojin ke ci gaba da samun nasara a kan 'yan kungiyar.

Ya kuma kara da cewa ko da yake dai cikin wannan lokaci kawo yanzu, ba a kawo karshen rikicin Boko Haram baki daya ba, amma fa an samu ingantuwar lamarin tsaron idan aka kwatanta da halin da ake ciki kafin zuwan gwamnatin.

A batun yaki da cin hanci da rashawa kuwa ya ce gwamnatin na daukar matakan da suka dace, ya kuma yi addu'a da fatan alheri.

Malamin na daya daga cikin shugabannin darikar Tijjaniya a kasar.