'Yan ci-rani: Sojojin Hungary na atiseye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata yar ci rani da yaromta sun tsaya a gaban 'yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Hungary

Sojojin Hungary sun soma atiseye a kan rawar da zasu taka nan gaba wajen samar da tsaro a kan iyakar kasar da ke kudanci domin rage yawan 'yan ci rani da ke kwarara cikin kasar.

Gwamnatin kasar na da anniyar tura sojoji domin su taimaka wa 'yan sanda a kan iyakar, inda dubban mutane ke isa Serbiya a kowacce rana.

Daga kasar ta Hungary, da dama daga cikin 'yan ci ranin kan doshi kasashe da ke arewacin Turai irinsu Austria da Jamus.

A daren Laraba 'yan gudun hijira sama da 3,000 suka tsallaka zuwa kasar ta Austria.

A wani labarin kuma, wani jirgin ruwa ya bar tsibirin Lesbos domin ya kwashe masu neman mafaka da ke cikin sansanonin da ke fama cunkuson jama'a zuwa birnin Athens.