ICC ta ba da sammacin kama 'yan Kenya

Image caption Babbar mai shigar da kara a ICC, Fatou Bensouda

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya watau ICC ta wallafa sammacin da ta yi amfani da shi wajen kama wasu 'yan kasar Kenya biyu da ake zargi da amfani da cin hanci wajen juya ra'ayin wasu shaidu.

An ba da sammacin domin kama Paul Gicheru da kuma Philip Kipkoech Bett ne a watan Maris, amma ba a wallafa ba sai yanzu.

Kotun ta ce, an kama mutanen biyu ne a watan Yuli.

Bara ne dai masu shigar da kara na kotun ta ICC suka janye tuhumar keta hakkin bil'adama da aka yi wa shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.

Amma mataimakinsa William Ruto da wani dan jarida har yanzu suna fuskantar tuhuma da ta shafi tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.