Dalibi mai shekaru 94 ya rasu a Kano

Hakkin mallakar hoto Abdulkarim Ibrahim
Image caption Margayi Malam Abubakar a cikin makaranta

Dalibin da ake dauka shi ne dan makaranta mafi tsufa a Nigeria ya rasu yana da shekara casa'in da hudu.

Malam Abubakar Muhammad Modibbo ya soma karatun Firamare ne yana shekaru fiye da tamanin, kuma ba da jimawa ba ya soma karatun sakandare a makarantar koyan harshen labarabci ta Kano watau SAS.

Bai samu damar zuwa makaranta ba a lokacin kuruciyarsa, saboda yana harkar kasuwanci, inda yake zuwa fatauci zuwa garuruwa daban-daban.

Malam Abdulkarim Ibrahim wani malami a makarantar da marigayin yake ya ce, Muhammadu Modibbo ya kasance mai saukin kai da ke hulda mai kyau da sauran 'yan makaranta.

"Tsakaninsa da yara kullum cikin raha yake, kuma yana daukarsu kamar abokansa. Kuma in ka je aji a lokacin da ake darasi, yana natsuwa sosai abin da bai gane ba sai ya tambayi malami ko kuma dalibin da ke zaune a kusa da shi," in ji Ibrahim.

Hakkin mallakar hoto Abdulkarim Ibrahim
Image caption Margayin tare da wani malami a makaranta

Margayi Abubakar Muhammad Modibbo ya rasu a ranar Litinin din da ta wuce sakamakon gajeruwar jinya kuma tuni aka yi jana'izarsa a Kano.