Gobara ta hallaka iyalan gida daya a Lagos

Image caption Gobarar ta lakume dakin kwanan mamatan

Gobara ta hallaka mutane bakwai iyalan gida daya a yankin Obele da ke jihar Lagos cibiyar kasuwancin Nigeria.

Gobarar wacce ta tashi cikin dare a ranar Laraba, ta janyo mutuwar mai gidan da uwargidansa da yara kanana da kuma wata dattijuwa.

Kawo yanzu ba a san musababbin gobarar ba, wacce ta kone gidan mutanen da ke lamba 23 a titin Michael Ogun na yankin Obele a Lagos.

A lokacin da masu kashe gobara suka isa gidan, sun tarar da mutanen duk sun rasu.

Wakilin BBC a Lagos ya ce mutane sun yi cincirundo a kusa da gidan suna jimamin wannan bala'i da ya auku.