Kaza marar kai a Amurka

Hakkin mallakar hoto LIFE GETTY IMAGES

Kimanin shekaru 70 da suka gabata, wani manomi a garin Colarado na kasar Amurka ya yanke kan wata kaza kuma ta ki mutuwa.

Kazar wacce ake kira Mike ta rayu har watanni 18 kuma ta yi fice sosai.

Amma ya ya aka yi ta dade a raye ba tare da kai ba ? in ji Chris Stokel-Walker.

A ranar 10 ga watan Satumbar shekarar 1945, Lloyd Olsen da matarsa Clara suna yanka kaji a gonarsu da ke garin Fruita a Colarado.

Olsen yana yanka kajin, matarsa kuma tana wanke su.

Amma daya daga cikin kajin, kimanin 50 din da suke shan wuka a hannun Olsen a ranar sai ta ba da mamaki.

A cewar jikan wadannan ma'aurata Troy Waters, wanda shi ma manonmi a garin Fruita, "Bayan sun kammala yanka kajin sai suka gano wata guda daya da bata mutu ba, ta kuma tashi ta ci gaba da tafiya."

Kazar ta ari takalmin kare ta zura da gudu kuma ba ta tsaya ba.

Christa Waters matar Troy ta kara da cewa "A wannan daren dai sai aka ajiye kazar a cikin wani tsohon akwati da ake ajiyar Tuffah watau Apple a gonar, da gari ya waye ko da Lloyd Olsen ya fito don ya duba halin da ake ciki, sai kawai ya ga kazar nan har a lokacin ba ta mutu ba. Wannan na daga cikin tarihin abin al'ajabi da ya taba faruwa da zuri'armu."

Troy dai ya samu wannan labari ne lokacin da yake yaro, lokacin da tsufa ya cimma kakansa ya zo yake zama da iyalan jikan nasa. Dakin Troy na kallon dakin da kakan nasa yake, kuma da yake tsohon ba ya samun bacci sosai, ya kan shafe tsawon sa'o'i yana zuba zance.

Hakkin mallakar hoto Waters Family
Image caption Wadannan sune Llyod Olsen da matarsa Clara masu wadanda suka yanka kazar a gonarsu

Troy ya ci gaba da cewa "Ya dauki yankakkun kajin domin ya sayar da su a 'yan kaji, ya tafi da zakaransa - kuma a wancan lokacin yana amfani da doki da kuma mota kirar wagon. Ya dauki kazar ya tafi da ita ya kuma fara cewa mutane in har za su bashi giya ko wani abu to zai nuna musu kazar da an fille mata kai amma har yanzu tana da rai."

Zancen wannan kaza mai ban al'ajabi ya bazu tamkar wutar daji a garin Fruita.

"Wasa a bainar jama'a"

Wata jarida ta tura wakilinta domin ya tattauna da Olsen, makonni biyu bayan da wani mai shirya wasanni a bainar jama'a Hope Wade, ya taho tun daga garin Utah kimanin kilomita 300 domin ya ga kazar.

Ya zo musu da wata shawara, inda ya ce su dauki kazar su yi wasa a bainar jama'a don su sami kudi.

Troy ya ce "gashi kuwa a wancan lokacin shekarun 1940, 'yar karamar gona kawai muka mallaka, suna faman fafutuka."

Da farko sun fara da ziyartar garin Salt Lake City da kuma jami'ar garin Utah, inda aka yi ta yin gwaje-gwaje da batira a kan kazar.

An yi ta jita-jitar cewa masana kimiyya na jami'ar sun cire kawunan kaji da dama domin su ga ko za su rayu.

A wannan lokaci ne mujallar Life ta yi fice sosai a kan labarin kaza mai ban al'ajabi mai rai babu kai.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Troy Walter jikan Llyod Olsen tsaye a jikin gunkin da aka yi don tunawa da kaza Mike

Daga nan kuma sai Lloyd da Clara da kuma Mike suka tafi Amurka domin yawon shakatawa

An ci gaba da bai wa kaza Mike abinci da ruwa ta inda ake zurara mata ta makogwaro.

A daren da Mike ta mutu, sun farka ne a dakin kwanansu na otal suka ji tana shakuwa.

Kafin su yi kokarin yin wani abu har Mike ta mutu.

Wani kwararre a harkar kaji Dr Tom Smulders, ya ce ya gano dalilin da yasa Mike bata yi saurin mutuwa ba, saboda bata zubar da jini sosai ba a lokacin da aka yanka ta.