'Fashi na karuwa a dajin Falgore'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an 'yan sandan na Nigeria na da babban kalubale a gabansu

Direbobin motocin dake ratsa dajin falgore a kan hanyarsu ta zuwa Jos daga Kano, sun koka da yawan fashi da makami da suke fuskanta a kan hanyar.

Direbobin sun ce janye shingayen sojojin da aka yi a titin da ya ratsa ta dajin, ya bai wa 'yan fashi damar cin Karen su ba babbaka kusan ko yaushe

Su ka ce hakan na jefa su cikin halin dar-dar a duk lokacin da zasu ratsa dajin.

To sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce za ta samar da jami'an tsaro a cikin dajin, domin magance yawan fashin da ake fuskanta.