Masana na tsokaci kan rage ofishin jakadanci

Image caption Shugaba Buhari na kokarin rage yawan ofisoshin jakadancin kasar da ke kasashen waje.

Masana harkokin diplomasiyya a Najeriya na ci gaba da tsokaci dangane da yunkurin shugaba Muhammadu Buhari, na rage ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje.

Yayin da wasu masana ke ganin rage yawan ofisoshin jakadancin kasar shi ne daidai, wasu kuwa na ganin akwai bukatar a kara yawan ofisoshin jakadancin Najeriyar ne a kasashen duniya.

Wani Malami a sashen nazarin hulda da kasashen duniya da manufofin raya kasashe a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, Malam El Haroun Muhammad, ya shaida wa BBC cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar kara yawan ofisoshin jakadacinta ne a kasashen duniya, amma ba a rage yawan su ba, saboda wasu dalilai.

Ya ce "Idan aka yi la'akari da halin da kasar nan ta samu kanta a ciki kafin hawan shugaba Buhari mulki da yadda ake kallonta a kasashen duniya, to batun ba na rage ofisoshin jakadanci ba be, na a duba irin mutanen da ake tura wa ofisoshin jakadancin ne."

A ranar Laraba ne shugaba Buhari ya bayyana cewa zai rage yawan ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen waje, bayan da babban Sakatare a ma'aikatar kula da hulda da kasashen waje na kasar ya yi masa jawabi a kan ayyukan ma'aikatarsa.