Makomar 'yan gudun hijirar Syria

Watakila wani abun dubawa kan hotunan 'yan gudun hijira daga kasar Syria da ke kwarara zuwa Turai shi ne, alamu ne da ke nuna akwai gagarumar matsala.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da alkaluma a makon da ya gabata, inda ta ce suna cikin kashi shida cikin 100 na yawan 'yan Syria da ke barin kasarsu.

Akwai wasu karin 'yan gudun hijira miliyan hudu a kasashe makwabta irin su Turkiya da Jordan da kuma Lebanon.

Akwai kuma wata kididiga da ke nuni da cewa akwai 'yan Syria sama da miliyan bakwai da suka rasa matsugunansu a cikin Syriar kuma ba'a san halin da suke ciki ba.

Bayan da mayakan 'yan tawaye su ka kwace ikon garin Idlib a watan Maris, mutane dubu 230,000 ne suka bar gidajensu zuwa wasu wurare ko yankuna da ke makwabtaka da garin.

Image caption Wasu daga cikin 'yan gudun hijira daga kasar Syria da ke wani sansani

.

"Rikici ya tarwatsa mutane"

Rikicin Syria ya tilastawa mutane da dama sauya matsuguni fiye da sau daya.

Iyalin karamin yaron nan mai shekaru uku Alan Kurdi, wanda ya rasu sun yi ta sauya matsuguni a cikin Syria kafin daga bisani suka yanke shawarar barin kasar baki daya.

Sun tashi daga Damascus babban birnin kasar Syria zuwa Aleppo daga nan kuma suka nufi Kobane.

Erin Mooney kwararriya ce a kan duba matsalar mutane da suka rasa muhallinsu, wadda kuma ta taba aiki a kasar ta Syria, ta ce "Da farko mutane kan yi kokarin shawo kan matsalar da suke ciki a kasar haihuwarsu."

Ta kara da cewa, "Su kan so su tsaya kusa da gidajensu domin su dinga sa ido a kan kadarorinsu, saboda suna fatan komawa gida watarana. Sai dai shekaru 5 kenan da barkewar tashin hankalin kuma mutane sun shiga mawuyacin hali."

Yan gudun hijira da ke tafiya Turai na da karfin barin Syria. Akasarin mutane da suka rasa muhalli masu karamin karfi ne idan aka kwatanta da 'yan gudun hijira da ke kwarara zuwa Turai.

" Tafiya zuwa Turai abu ne mai wahalar gaske, kuma kana bukatar kudi", a cewar Carsten Hansen , Darakta a cibiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway a yankin Gabas ta Tsakiya.

Halin da mutanen da suka rasa muhalinsu ke ciki a cikin Syria abu ne da ba a gani a kafofin watsa labarai saboda wurare ne masu hadari sosai ga 'yan jarida da ke son su shiga.

Akwai dokar da ke samar da kariya ga 'yan gudun hijira da ke barin Syria zuwa kasashen waje, karkashin yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma a shekarar 1951 a Majalisar Dinkin Duniya wadda ta nemi kare musu hakokinsu.

Wadanda aka bari a can kasar Syria kuwa, a gefe guda a hukumance suna samun kariyar gwamnatin shugaba Bashar al Assad, kuma ga 'yan gudun hijira da dama gwamnatinsa ce ta jefasu cikin halin kuncin da suka shiga yanzu.