An samu shaidar harin makamai masu guba a Syria

Wani da harin gubar Chlorine ya ya shafa a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani da harin gubar Chlorine ya ya shafa a Syria

BBC ta samu shaidar dake nuna cewa a Syria an kai hari fiye da sau sittin da makamai masu guba tun bayan majalisar dinkin duniya ta bada umarnin lalata makamai masu guba da Syrian ta mallaka shekaru biyu da suka gabata.

An zargi dakarun shugaba Assad da sakin sanadarin Chlorine mai hade da gas ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu. Wakilin BBC ya ce, akwai dai hanyoyi da dama na samun sanadirin Chlorine ga bangarorin dake yaki da juna a Syria. Kuma sinadarin Chlorine din ba a haramta shi ba, amma ana mayar da shi makami.

Akwai dai zargin cewa, mayakan kungiyar IS sun yi amfani da samfurin wata guba sau biyu wajen kai hare-hare.

Shaidu a kauyen Maraa sun fadawa BBC cewa, 'yan kungiyar IS ne suke kai hare-haren da guba.

Majalisar dinkin duniya ta kaddamar da bincike dan gano ko su waye, ko wacce kungiya ce, ko gwamnati ke kai hari da makamai masu guba a yakin Syria.