Kotu ta samu mutane 12 da laifin kai harin Mumbai

Image caption Zakiur Rahman na cikin mutanen da ake zargi da kai harin Mumbai.

Wata kotu a kasar Indiya ta samu mutane 12 da laifi a harin da aka kai a birnin Mumbai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 280.

Kotun ta kuma wanke mutum daya.

An kai harin ne da bama bamai guda bakwai a tashar jiragen kasa a shekarar 2006, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.

Gwamnatin Indiya ta zargi kungiyar Lashkar-e-Taiba ta kasar Pakistan, wadda ke ikirarin kishin Musulinci, da kai harin koda yake gwamnatin Pakistan ta musanta zargin.

An samu mutanen 12 ne da laifin kaddamar da yaki a kan wata kasa, da kutungwila da kuma kisan kai.

A ranar 14 ga watan Satumba za a yanke musu hukunci.