Mutum daya ya rasu a rikicin Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla mutum guda ne ya rasu a wata zanga-zangar da aka yi a kasar Ivory Coast.

Masu zanga-zangar suna nuna kyama ga tsayawa takarar da shugaban kasar Alassane Ouattara ya yi a zaben da za a yi a watan gobe.

Kazalika an halaka mutum daya tare da kona gidaje da dama a jihar yammacin kasar, haka kuma an yi dauki-ba-dadi a Abidjan, babban birnin kasar.

'Yan adawar kasar ne suka shirya zanga-zangar kyamar takarar Alassane Ouattara da wasu 'yan takarar tara da kotun tsarin mulkin kasar ta amince da su.

Daga cikin 'yan adawar har da wasu magoya bayan tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wanda ke zaman wakafi a kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague.