Direbobin manyan motoci na yajin aiki

Image caption Yajin aikin Manyan motoci a Legas zai iya shafar karancin kayan abinci

Direbobin manyan motoci masu dakon kayayyaki a Legas sun fara yajin aiki bayan da aka tashi baram baram a tsakanin wakilan gwamnatin jihar da kuma na masu manyan motocin.

Direbobin da suka hada da masu dakon man fetur da kuma trailer-trailer sun ce sun dauki matakin janye motocinsu domin kin amincewa da umarnin gwamnatin Legas na hana su tafiya a kan hanyoyin jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe tara na dare na kowacce rana.

Direbobin sun yi korafin cewa suna fuskantar barazanar tsaro saboda haka aiki da daddare ba zai yiwu ba.

Wannan yajin aikin zai sa a fuskanci matsalar karancin kayan abinci da ake shigowa da su cikin birnin ko jigilar su a cikin jihar.