Palasdinawa sun yi maraba da kuri'a mai cike da tarihi

Hakkin mallakar hoto AFP

Palasdinawa sun yi maraba da abinda suka kira wata kuri'a mai cike da tarihi da MDD ta kada, wacce ta basu damar kafa Tutarsu tare da sauran mambobin kasashe a wajen ginin Majalisar dinkin duniyar.

Wakilin Palasdinawan a Majalisar dinkin duniya Riyad Mansour ya ce sanya tutar ba zai kawo karshen mamayar da Israila ta ke mu su ba.

Sai dai ya ce ya dauki hakan a matsayin wata alama ta goyan bayan da kasashen duniya ke basu,game da tafiyar Palasdiwan ta neman kafa kasarta

A dayan bangaren kuwa jakadan Israila a Majalisar dinkin duniya, Ron Prosor, ya bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri da babu komai a cikinsa.

Ya ce ta hanyar tattaunawa ce kadai Palasdinawa zasu iya samun yanci cin gashin kai.