Za a kafa tutar Falasdinu a ginin MDD

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Falasdinawa na murna kan wannan matakin

Falasdinawa sun yi maraba da abin da suka kira wata kuri'a mai cike da tarihi da Majalisar Dinkin Duniya ta kada, wacce ta basu damar kafa Tutarsu kamar sauran mambobin kasashe a wajen ginin Majalisar.

Wakilin Falasdinawan a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour ya ce sanya Tutar ba zai kawo karshen mamayar da Isra'ila take musu ba.

Amma ya dauki hakan a matsayin wata alama ta goyan bayan da kasashen duniya ke basu, game da fafutukar Falasdiwan ta neman kafa kasarta.

Amma jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Ron Prosor, ya bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri da babu komai a cikinsa.

Prosor ya ce "Babu wata kuri'a da za ta iya juya wani yunkuri da babu komai a cikinsa zuwa kasancewa wata kasa. Dole ne kasashen duniya su nuna wa Falasdinawa karara cewa hanyar samun kasarsu, ita ce tattauna ta kai tsaye."