Mutane 87 sun rasu a Masallacin Ka'aba

Hadari a masallacin Ka'aba a kasar Saudia Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hadari a masallacin Ka'aba a kasar Saudia

Mutane fiye da tamanin ne suka rasu a masallacin Ka'aba da ke Makka a Saudiyya bayan da injin na daga kayan gine-gine ya fado kasa.

Wasu kuma fiye da dari da tamanin kuma sun sa samu raunuka, kuma an garzaya da su asibiti

Wasu hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna mahajjatan da ke kwance jina-jina, kana ga wasu sassan injin daga kayan da ya fado ta cikin rufin silin.

Injin din ya fado ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara.

Lamarin ya faru 'yan makonni kafin gudanar da Arafa a yayinda maniyyata daga kasashe daban-daban na duniya suka hallara a kasar domin sauke farali.

A bara ne kasar ra Saudia ta kayyade yawan adadin mahajjatan saboda ayyukan gine-ginen a babban Masallacin na Ka'aba.