Mutane 52 sun rasu a Masallacin Ka'aba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadanda suka jikkata an kai su asibiti

Mutane fiye da hamsin sun rasu a Masallacin Ka'aba da ke Makka a Saudiyya bayan da injin na daga kaya ya fado kasa.

Injin din ya fado ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sharara.

Hukumomi a Saudiyya sun ce a kalla mutane 30 sun rasu sakamakon hadarin.

Lamarin ya faru 'yan makonni kafin gudanar da Arafa a yayinda maniyyata daga kasashe daban-daban na duniya suka hallara a kasar domin sauke farali.