Masar: Majalisar ministoci ta yi murabus

Ɗaukacin 'yan majalisar ministocin gwamnatin Masar sun miƙa takardun su na murabus ga shugaban ƙasar Abdel Fatah al-Sisi.

Babu wata sanarwa da aka bayar a hukumance kawo yanzu dangane da batun.

Sai dai an ruwaito cewa shugaban kasar bai gamsu da ayyukan da dama daga cikin ministocin ba.

Masu sharhi a kafofin yaɗa labarai sun zargi gwamnatin da rashin iya aiki da kuma badakalar cin hanci.

Ko da a wannan makon an tsare ministan ayyukan gona kan zargin cin hanci.

Shugaban kasar ya buƙaci Sharif Ismail wanda ke aiki a matsayin albarkatun mai da ya kafa sabuwar majalisar gudanarwa cikin mako ɗaya.