'Yan Nigeria uku ne suka jikkata a Makka

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta ce babu ko daya daga cikin mahajjatan kasar da ya rasu sakamakon hadarin rikitowar babbar kugiyar daukan kayan gine-gine akan mahajjata a Saudiya.

Sai dai shugaban hukumar, Alhaji Abdullahi Muktar, ya ce mutane uku ne 'yan Najeriya suka jikkata sakamakon hadarin.

Ya ce mutanen sun hada da biyu maza da daya mace, sannan mahajjata ne daga jihohin Kaduna da Gombe.

Sai dai mai yiwuwa adadin 'yan Najeriya da suka jikkata ya haura uku, domin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, daga jihar ta Sokoto yana daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa.

Alhaji Attahiru Bafarawa wanda ya shaidawa BBC yadda lamarin ya ritsa da shi, ya ce ya samu sauki kuma tuni aka sallame shi daga asibiti.

Hukumomi a Saudiya sun dauki mataki da zai bai wa mutanen da ke kwance a asibiti sakamakon hadarin damar yin hawan Arfa.